Matthew 14

1A lokacin nan ne, Hiridus mai mulki ya ji labarin Yesu. 2Ya ce wa barorinsa, “Wannan Yahaya mai baftisma ne; ya tashi daga matattu. Saboda haka wadannan ikoki na aiki a cikinsa”.

3Domin Hiridus ya kama Yahaya, ya daure shi, kuma ya jefa shi a kurkuku saboda Hirudiya, matar dan’uwansa Filibus. 4Ya ce masa, “Bai kamata ka dauke ta a matsayin matarka ba.” 5Da Hirudus ya kashe shi, amma yana tsoron jama’a, domin sun dauke shi a matsayin annabi.

6Amma da ranar bikin haihuwar Hirudus ta kewayo, diyar Hirudiya tayi rawa a lokacin har ta burge Hirudus. 7Sai ya yi mata alkawari har da rantsuwa cewa ta roki komenene ta ke so, zai ba ta.

8Bayan ta amshi umurni daga wurin mahaifiyarta, ta ce, “Ka bani kan Yahaya mai baptisma a kan tire. 9Sarki ya husata da rokonta, amma domin rantsuwar da ya yi kuma domin mutanen da ke a wurin bukin tare da shi, sai ya umurta a yi haka.

10Ya aika aka yanke kan Yahaya acikin kurkuku. 11Sai aka kawo kansa bisa tire, aka mika wa yarinyar, ta kuwa kai wa mahaifiyarta. 12Sai almajiransa suka zo, su ka dauki gawar su ka je su ka yi jana’iza. Bayan haka, su ka je su ka fada wa Yesu.

13Sa’adda da Yesu ya ji haka, ya fita daga cikin kwale-kwale zuwa wani kebabben wuri. Da taron suka ji haka, suka bi shi da kafa daga biranen. 14Sai Yesu ya zo gabansu, ya kuma ga babban taron. Ya tausaya masu ya kuwa warkar da marasa lafiya dake cikinsu.

15Da maraice ya yi, almajiransa su ka zo su ka ce masa, “Wannan wuri jeji ne, dare kuwa ya riga ya yi. Ka sallami taron domin su je cikin kauyukan nan, su sayo wa kansu abinci.”

16Amma Yesu ya ce masu, “Babu amfanin tafiyar su, ku basu abin da za su ci.” 17Suka ce masa, “Muna da gurasa guda biyar da kifi biyu ne kawai.” 18Yesu ya ce, “Ku kawo mani su.”

19Sai Yesu ya umarci taron su zauna akan ciyawa. Ya dauki gurasa biyar da kifi biyun. Ya dubi sama, ya sa albarka ya gutsuttsura ya kuma ba almajiran. Almajiran suka ba taron. 20Dukansu suka ci suka koshi. Sai suka dauki gutsattsarin gurasa da kifin, kwanduna goma sha biyu cike. 21Wadanda su ka ci kuwa kimanin maza dubu biyar ne, ban da mata da yara.

22Nan take sai ya sa almajiran suka shiga kwale-kwalen su haye zuwa dayan gefen kafin shi, domin ya sallami taron. 23Bayan ya sallami taron sun tafi, sai ya haura kan dutse domin yayi addu’a. Da dare yayi, yana can shi kadai. 24Amma yanzu fa kwale-kwalen na tsakiyar tekun, kuma da wuyar sarrafawa saboda rakuman ruwa da iska na gaba da su.

25Da asuba (wajen karfe uku na dare) Yesu ya nufo su yana tafiya akan teku. 26Da almajiran suka ganshi yana tafiya akan tekun, sai suka firgita suna cewa, “Fatalwa ce,” suka yi kururuwa cikin tsoro. 27Amma Yesu yayi magana da su nan da nan yace, “Ku yi karfin hali! Ni ne! Kada ku ji tsoro.”

28Bitrus ya amsa masa cewa, “Ubangiji, idan kai ne, ka umarce ni in zo wurin ka bisa ruwan.” 29Yesu yace, “Zo” Sai Bitrus ya fita daga jirgin yana tafiya akan ruwan zuwa wurin Yesu. 30Amma da Bitrus ya ga iska, sai ya tsorata. Yayin da ya fara nutsewa, sai ya tada murya ya ce, “Ubangiji, ka cece ni!”

31Nan take Yesu ya mika hannunsa, ya kama Bitrus ya ce masa, “Kai mai karancin bangaskiya, meyasa ka yi shakka?” 32Bayan da Yesu da Bitrus suka shiga cikin kwale-kwalen, sai iska ta daina kadawa. 33Sai almajiran dake cikin kwale-kwalen su ka yi wa Yesu sujada suna cewa, “Hakika kai Dan Allah ne.”

34Da suka haye, sun iso kasar Janisarata. 35Da mutanen wurin suka gane Yesu, sai suka aika da sako zuwa dukan yankin, kuma suka kawo masa dukan marasa lafiya. Suka roke shi don su taba gezar rigarsa, kuma dukan wadanda suka taba shi sun warke.

36

Copyright information for HauULB